Ads

Wasiyyar Wani Bawan Allah Ga Dansa

0

- Advertisement -

Ya Kai Dan Uwa Maabocin Karatu Kayi Kokarin Karnta Wannan Nasiha Domin Kuwa Kai Kanka Zata Amfane Ka Sosai

Alummarhausa.com.ng

  • YA KAI DANA!

Ka sani cewa, watarana tsufa zai kama ni. Zan riqa yin abubuwa ba yadda aka saba ba. Ka sa haquri sosai don ka fahimce ni.

Related Posts
1 of 9
  • YA KAI DANA!

Idan wancan lokacin ya zo hannuna zai kasa riqe abinci, sai yana zuba a kan tufafina.

Zan kasa cire ma kaina tufafi bayan na lalata su ballai in iya sanya wasu. Ka yi haquri da ni. Ka tuna lokacin da na koya maka abinda yanzu na kasa iyawa.

A wannan lokaci zan kasa yin tsafta yadda kake buqata. Kada ka manta ni ne na koya maka yin tsafta da kwalliya da shafa turare.

Kada ka yi dariya idan ka ga ina yin wauta, ko na kasa gane abubuwa yadda ya kamata. Ka zama kai ne qwaqwalwata da idona da kunnuwana don in gane abubuwa.

Ka tuna cewa, ni na koya maka zaman duniya da yadda ake jin dadin rayuwa. Don me ba za ka yi haquri idan na buqaci wannan koyarwar ka koya min ba?

Idan lokacin da nike fadi ya zo tunanina zai yi rauni, qasusuwan jikina za su yi sanyi, harshena zai yi nauyi. A lokacin kuma babu abinda nake so sai kusancinka da jin duriyarka. Yi qoqari ka taimaka min don biyan buqatata. Ko a wannan lokacin na san abinda nike so a raina kodayake ba lalle ne in iya fada maka ba.

Muhimman Batu
1 of 2

Alummarhausa.com.ng

  • YA KAI DANA!

Idan qafafuna suka kasa dauka ta, ka tuna lokacin da na riqa daukar ka har hannayena su yi sanyi. Idan na so ka sauka sai ka ce ba ka sauka. Ni kan yi ta rarrashinka a wancan lokaci don in samu yardarka. Kada ka ji kunyar riqa hannuna ko runguma ni a wannan lokaci. Watarana kai ma za ka buqaci mai yi ma ka haka.

  • YA KAI DANA!

Idan na tsufa zan daina fahimtar al’amurran duniya yadda ya kamata. Zan riqa jiran mutuwa ne a kowane lokaci. Kada ka gajiya wajen taimako na domin wata babbar kofar aljanna ce Allah ya bude maka.

  • YA KAI DANA!

Idan ka tuna wani laifina a gare ka, ka iya fahimtar cewa, ban yi shi don in musguna maka, ko in qetace ka ba. Na yi ne don in koya maka zaman duniya da yadda za ka zama cikakken mutum.

A yau babban abinda za ka yi min shi ne ka manta da kurakuraina, ka yafe laifukana. Ina fatar Allah ya yafe naka kurakurai, ya gafarta laifukkanka.

  • YA KAI DANA!

A lokacin da mahaifiyarka ta haife ka, ni ne na runguma ka, na kula ka, na dauki nauyin ka, na yi tarainiya da kai. Ka saka min a lokacin tsufa gabanin mutuwa ta.

Daga qarshe, ina sanar da kai cewa, dadai ba ni da farin cikin da ya fi jin dadinka, da ganin farin cikinka da murmushinka. Kada ka bari idan zan bar duniya in bar ta da baqin cikinka ko bacin rai a kan ka.

Allah ya yi maka albarka, ya sa ka gama da ni lafiya, ka samu wadatar arziki da jin dadin rayuwa, kuma ya ba ka wanda zai jibince ka idan naka lokaci ya zo.

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.