Ads

YIN MURMUSHI DA SAKIN FUSKA IBADA NE

0

- Advertisement -

YIN MURMUSHI DA SAKIN FUSKA IBADA NE

Alummarhausa.com.ng

Daga cikin sunnonin da aka Manta da da ita akwai SAKIN fuska da murmushi ga yan uwa a lokacin haduwa da juna, da yawa daga mutane suna aikata hakan amma basu dauki hakan ba a matsayin Ibada ba, amma hakan baya sanya wa su sami lada, har sai idan sun sanan yin hakan ibadane kuma Manzo Allah SAW ya kwadaitar, sai suka aikata hakan tare da kwadayin samun lada a wajen Allah da kuma koyi da biyayya ga Manzon Allah Saw, to a wannan lokacin suna da ladar Ibada da koya da Manzon Allah Saw.

Muhimman Batu
1 of 2

Alummarhausa.com.ng

Daga Abu Zarrin Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ :yace dani:
(Kada ka raina ayyukan alkhiri komai kankantarsa, ko da ka hadu da dan uwanka ne kayi masa murmushi da sakin fuska)
@صحيح مسلم – رقم : (2626)

Related Posts
1 of 9

Daga Jabir Dan Abdullahi Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah Saw yana cewa:
(Kowane kyakkyawan aiki da kyakkyawan abu sadaka ne, yana daga cikin kyakkyawan aiki sakin fuska da murmushi lokacin haduwa da juna)
@صححه الألباني في صحيح الترمذي – رقم : (1970)

        Allah ne mafi sani

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.