YADDA AKE HADA SPRING ROLLs DA MEAT PIE
yadda ake Spring rolls da yadda ake meat pie
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu a yau inshallahu kamar yadda taken wannan pos din ya gabata zamuyi Magana ne akan yadda ake spring rolls ne da uka yadda ake hada meat pie, kamar yadda kowa ya sani suna daga dangin snacks ne, kuma ana yawan cinsu saboda dadinsu ya danganta na sayarwa ne, na ci gida ne ko ma na amare ne, to inshaallahu zamuyi bayani gamsashe akan yadda ake yin su tahanyar lissafa kayan da ake amfani das u da kuma yadda ake hada kayan amma da farko zamu fara Magana ne akan yadda ake spring rolls sannnan muje ga yaddda ake wato aynafn shi meat piea din.
Yadda ake Spring rolls
Shi dai spring rolls ana hada shi ne da wadannan kayayyaki da zamu lissafo a kasa wadanda sune zaa sawo a kasuwa domin a hada shi kuma a tsaftacesu sosai don a samu ingancin abinda akayi.
Kabeji 1/6
Nikakken nama
Karas
Mai
Albasa
Magi
Filawa kofi 2
Gishiri
Kwai 2
Buroshi (irin na cikin girki zaa samo).
Yadda zaa hada kayan
Dafarko dai zaa yayyanka tsaftataccen kabeji da karas da albasa sai a soya su ahankali wato sama sama tare da mai misalign cokali daya sai kuma a zuba dakakken ko nikakken nama, a sa magi da gishiri da curry harma da abunda ake so don ya kara masa armashi sai a sauke su baccin an dan soya su akan wuta.
Baccin an kammala mata na daya sai yanzu muje zuwa mataki na biyu inda zaa shafa filawa da kwai da magi da gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kaurin koko, a shafa mai cikin kwanon tuya sai a sa filawa da brushin fanti, bayan akalla kamar minti daya haka sai a cire daga kan wuda sai a zuba.
Wannan shine to yanzu kuma zameje ga yadda ake meat pie.
Yadda ake meat pie
Shima meat pie ana hada shi ne da wadannan kayan da zamu lissafa a kasa wadanda zaa nemo a kasuwa.
- Butter
- Gishiri
- Filawa
- Albasa
- Seasoning
- Karas
- Curry
- Peas
- Kwai
- Baking powder
- Meat
Yadda ake hadawa
A hada filawa,gishiri, curry, baking powder sai a sa butter ayi mixing dinsu sosai sai a sa kwai ayi mixing da ruwa sai a samu dambun idan ba zai kwansoya. sai a sa kayan lambu don yana kara masa dadi sosai, zaa yi grating din albasa a greater a yanka karas kanan a sa peas a rowan zafi yadan jima sannan sai a dauko duka a hada a dambun nama ana yi dan kara kayan dandano idan ana bukata. Idan aka yi haka sai a samo folk a daddane bakin idan kuma ana da abun meat kuma sai ayanka rawun - dashi a sa naman sai a kasa ko a soya
- To anan ne muka zo karsen wannan post din kuma muna fatan zaa cikaba da kasancewa da mu a wannan website mai aalbarka