FADAKARWA: ABOKIN HIRA 2
Wanda ya kunshi fadakarwa tare da nishadantarwa.
Darasi na 2
Darasin namu na yau shine Kwadayi Mabudin Wahala
Dija wata yarinya ce ‘yar gidan Idi mai haqa rijiya.
Tana da kyawonta daidai gwargwado, ga ta da farin jini a tsakanin ‘yan mata. Watarana ta je ziyarar zumunci a wurin wata qawarta ‘yar masu hali da zarafi sosai. A daidai qofar gidan da za ta shiga sai wani matashi mai lokaci ya zo wucewa, ana ce masa Danladi. Da ya kalle ta sai ta ba shi shawa, ya taka birki ya nemi yin magana da ita. Ta fada masa sunanta da sunan mahaifinta.
Da ya tambaye ta ko nan ne gidansu? Sai ta amsa masa da cewa, eh. Ya karbi lambar wayarta kuma ya yi mata alqawarin dawowa gobe.
Soyayya ta qullu a tsakanin su cikin qanqanen lokaci. A duk sadda yake son haduwa da ita sai ya kira ta ya sanar da ita sannan ya zo ya same ta a nan gidan a matsayin nan ne gidan iyayenta. Bai sani ba a she zuwa take yi ne lokacin da suka yi alqawari.
Ita kuma ‘yar talakawa ce, mahaifiyarta tana toya qosai a bakin tashar mota kuma ita ma takan taya ta yin wannan sana’ar wani lokaci.
A kwana a tashi, watarana ya buqaci su hadu da ita amma bai same ta a waya ba.
Sai qaddara ta debe shi ya nufi gidansu da suka saba haduwa, ya nemi wani yaro ya ce ya sallamo masa Dija. Yaro ya ce, ai ba ta zo ba. Daga ina? Yaro ya ce, daga gidansu.
Ina ne gidansu? Ya ce, mu je in kai ka. Danladi ya bi shi cikin al’ajabi tiryan tiryan sai qofar gidan su Dija. Da suka je yaro ya zarce zuwa cikin gida, jim kadan ya fito ya ce, ba ta nan amma an ce tana wurin sana’arta. Yaron kuwa ya yi masa tayin su je can.
Ko da suka tafi sai ga ta a tashar mota, almajirai da ‘yan tasha masu sayen kunu da qosai bayan la’asar sun yi mata zobe. Da suka yi arba da ita sai duk inda gashin jikinta yake ya tashi, hankalinta ya fice daga jikinta. Jin nauyi da rashin sanin yadda za ta kalli Danladi ya sa ta auna da gudu zuwa gida.
Cikin natsuwa Danladi ya bi ta har gida ya sallama ma mahaifinta wanda ya yi na’am da zuwan sa. Bayan sun dan tattauna sai ya fahimci cewa, lallai dattijon ya san da irin badaqalar da ‘yarsa take shiryawa, amma dai shi mabuqaci ne da ‘yan kudin da take samowa wurin Danladi suke taimaka masa wajen ta fi da rayuwar iyalinsa.
Danladi ya ce masa, to babu damuwa Baba. Ni daman ina son ta ne a tsakani da Allah kuma so na hada zumunta. Kuma ba da jimawa ba zan turo magabatana don su yi magana da kai. Amma a gaskiya zan ji nauyi a irin matsayina da na iyayena a tarar da gidan surukaina a cikin wannan yanayi. Don haka, zan turo ma’aikata a rusa wannan gidan naka na laka in gina maka sabo irin na zamani, sannan sai in aiko iyayena su zo su gan ka. Bayan haka ya kawo dan na goro ya ba shi. Malam Idi ya koma gida a cike da murna da jin dadi.
To, abin da yake faruwa dai, tuni an yi wa gidan su Dija rusau, ya koma fili fallau.
Danladi kuma ba a sake jin duriyarsa ba
Darasi
- Katsaya iya maysayin da Allah ya ajiyeka.
- Aguji yaudara
Ajiye mana wani darasi daka fahimta a wannan labari.