Ads

FADAKARWA: ABOKIN HIRA 1

0

- Advertisement -

ABOKIN HIRA LABARI NE DA YA KUNSHI FADAKARWA TARE DA NISHADI

Alummarhausa.com.ng

Darasi na 1

Taken shirin na yau shine Dogaro ga Allah Jari……..

Related Posts
1 of 9

Wata rana wani Sarki yana zaune a cikin lambunsa sai ya ga wata kyakkyawar Mace tana wucewa ta gefen lambun. Sai ya tura wasu daga cikin dogaransa don su ga gidan da wannan matar take. Da suka gama bincike akan matar sai suka dawo suka gaya ma Sarki cewa, wannan matar wani kafinta ne da yake garin. Sarki bai bata lokaci ba ya tura aka kirawo masa kafinta. A lokacin da dogari ya gaya ma Kafinta cewa Sarki yana son ganin sa sai jikinsa ya yi sanyi sosai saboda ya san halin Sarkin.

Ya tambayi dogari me ya sa Sarki yake nema na? Dogari ya ce masa, idan ka je wurin

Sarki ai za ka ji me ya sa yake nemanka?

Kafinta ya hadiye ransa, ya kama hanya ya je gidan Sarki, ya fadi ya yi gaisuwa. Sarki

ya daga kai ya kalle shi sama da qasa, sannan ya tambaye shi “me ye sana’arka?”

Kafinta ya ce: Ran Sarki ya dade ni Kafinta ne tun sama da shekaru ashirin nake

wannan sana’a. Sarki ya ce masa, ina so ka ciko min buhu bakwai da diddigar katako,kuma nauyin kowane buhu yakai Kilo dari daya, ka tabbata ka kawo min su gobe da safe. Idan kuwa har gari ya waye ba ka kawo ba, to zan sa a fille kanka.

Muhimman Batu
1 of 2

Alummarhausa.com.ng

Kafinta ya koma gida a cikin damuwa da fargaba da zullumi. Ya kuwa kasa bacci ko na daqiqa daya. Ya riqa juye juye a kan shifid’arsa saboda ya san qaryarsa ta qare tun da ba zai iya biya ma Sarki buqatarsa ba. Da matarsa ta ga yanayin da yake ciki sai ta tambaye shi, me yake faruwa ne? Ya kwashe duk labarin ya fada mata. Yace, kin ga kuwa ai ni kam rayuwata ta zo qarshe kenan. Sa’annan ya fashe da kuka.

Matarsa ta rarrashe shi tana ba shi haquri. Ta ce masa, ka yi bacci abinka. Rayuwar kowa a hannun Allah take, kuma zai iya rufa mana asiri idan muka yi tawakkali a

gare shi.

Gari ya waye Kafinta bai dandani bacci ba ko na sisin kwabo saboda tsoro. Da sassafe sai ya ji ana kwankwasa kofar gidansa. Ya firgita matuqa, ya ce da matarsa, ni kam tawa ta qare, ina roqon ki gafara, sai mun hadu a Darassalami. Ya yi jarunta amma fa a cikin fargaba, ya zo bakin qofa ya ce, wa ye? Aka ce masa, dogarin Sarki ne, ka bude

Kofa. Ya hadiye ransa, jiki na bari ya bude kofar. Ko da suka yi ido hudu da dogari sai ya ce masa, ka taimaka ka bude shagonka a yanzu muna son ka qera mana makara a cikin gaggawa, domin Allah ya yi ma Sarki cikawa. Da farko Kafinta bai yarda da maganar da ya ji ba sai da ya ga cewa, haqqan dogarin da gaske yake yi, sannan ne farin ciki ya lullube shi.

Dogari ya ce masa, ka yi amfani da katako mai kwari sosai, ko nawa ne ma kake so zamu biya ka. Kafinta ya ce, ai yallabai tun da mai martaba ne ya cika ni ko sisin kwabo ma ba ni buqata.

Darussa:

  • Wanda ya mayar da lamarinsa ga Allah, Allah ya ishe shi.
  • Zalunci mugun jari
  • Hattara da hawayen wanda ka zalunta

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.