Ads

FALALAR YIN SALATI GA MANZON ALLAH (SAW)

0

- Advertisement -

SALATI MAI DUBUN ALBARKA

Alummarhausa.com.ng

Wani bawan Allah ne ya gamu da jarrabawa. Daman dai shi dan kasuwa ne, yana saye da sayarwa. Sai aka jarabce shi da kariyewar arziki da durqushewar jari.

Ga shi kuma bashi ya taru mai yawa a kan sa. Dole ta sa shi cin bashin wani attajiri marar uzuri wanda ba ya sassafci balai tausayi. Ya ari kudinsa wuri na gugar wuri har Dinari dubu biyar da irin kudinsu na zamani dauri. Da lokacin biya ya yi kuma abin bai samu ba sai attajirin ya kai shi qara wajen Alqali.

Related Posts
1 of 9

Bai musanta kudin da ake bin sa ba amma ya tabbatar ma Alqali cewa, babu su kuma babu hanyarsu. Don haka, Alqali ya yanke masa hukuncin dauri na shekara biyu ko kuma har sadda kudi suka samu. Jin haka, wannan bawan Allah ya roqi Alqali ya ba shi damar zuwa ya kimtsa gidansa kuma ya sanar da iyalansa a cikin kwana guda. Alqali ya amince.

Ya ce, amma ka zo da wanda zai karbi belinka. Sai mutumin ya kada baki ya ce, Annabi Muhammadu ne Sallallahu Alaihi wa Sallam zai yi beli na. alqali ya ce, kamar ya ya?

Ya ce, ka ba da beli kawai ga Annabi, idan ban kawo kaina ba gobe ba ni cikin al’ummarsa. Alqali ya yi nazari jim kadan, sannan ya ce, ba komai. Ka tafi mun ba da belinka ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Sallam. Mutumin ya kama hanya ya tafiyarsa.

Da ya isa gida sai ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya fada ma matarsa.

Sai matar ta ce, ashe kuwa tun da Annabi ne aka ba shi belin mu ya dace mu zauna mu yi ta yi masa Salati har in da gari ya waye. Suka kuwa zauna bayan sallar lisha suka yi ta Salati ga Annabi har inda bacci ya kwashe su.

A cikin baccin sai wannan bawan Allah ya yi mafarkin Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam yana ce masa, idan ka wayi gari ka je wurin Sarki ka ce masa na ce ya biya maka wannan bashin shi kuma Allah zai yaye masa damuwa ranar Alqiyama. Idan ya tambaye ka alama ka ce na gaya maka kullum yana yi min Salati dubu daya amma jiya yakasa saboda bacci ya kwashe shi.

Amma fa Allah ya rubuta masa ladar aikin nasa cikakke kamar yadda ya saba yin sa. Da aka wayi gari ya je wurin Sarki ya isar da wannan saqo sai Sarki ya yi farin ciki matuqa da jin wannan batu don ya haqiqance lallai da gaske ne ya ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam a cikin mafarki, kuma mafarkin Annabi gaskiya ne. Nan take Sarki ya sa aka kawo masa Dirhami dubu biyar na biyan bashi, sannan da wasu dubu biyar don ya yi jari albarkar wannan bushara da ya zo masa da ita.

Muhimman Batu
1 of 2

Alummarhausa.com.ng

Wannan bawan Allah bai garzaya ko ina ba sai wurin Alqali. Da isar sa sai ya isko Alqali zaune yana jiran sa. Ya tarbe shi a cikin murna ya ce, tun da safe kai nike jira. Ga kuma Dirhami dubu biyar nan na ba ka ka biya bashin da ake bin ka. Domin ban taba mafarkin Annabi ba sai a yau na yi shi albarkacinka kuma ya gode min da na ba shi belinka.

Suka zauna suna jiran Attajiri don ya zo a sallame shi. Jim kadan sai ga shi ya iso a cikin gaggawa da jakar kudi a hannunsa. Ya ce, Allah ya dade ran Alqali bashi dai da nake bin sa na yafe masa. Sannan kuma ga wasu Dirhami dubu biyar nan

albarkacin mafarkin Annabi da na yi ya nemi in yafe masa.

Da haka wannan bawan Allah ya koma gida babu bashi a kan sa, kuma ga wani sabon jari na Dirhami dubu ashirin Allah ya ba shi albarkacin Salati.

Babu shakka, Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi gaskiya da ya ce ma wanda ya ce zai mayar da nafilarsa gaba daya ta koma Salati. Sai Annabi ya ce masa, “Idan ka yi haka Allah zai yaye maka duk damuwarka, sannan ya yafe zunubanka”.

Darussa:

  • Salati maganin matsaloli ne, mai yaye damuwa
  • Kada ka damu idan ka shiga wani hali. Duniya juyi ce.
  • Wanda ya yaye damuwar dan uwansa Allah zai yaye masa tasa.
  • Da yawa lokutan da muke batawa, da mun cika su da Salati da mun yi riba

Yadan Uwa Mai Albarka Allah yabaka ikon Turawa wani Group Din Amin.

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.