NASIHA AKAN WAYOYINMU 📱📱
Waya wata aba ce da Allah ya jarabci mutanen wannan Zamanin da ita…. Ta inda zaka samu Abu ne mai wahala ga mafi yawancin mutanen wannan zamani su yi Minti 30 basu danna wayarsu ba.
Kusan kowa yanzu waya ta zame masa Jiki.
📱Ita ce abar da muke tabawa a qarshe kafin mu kwanta
📱Ita ce abar da muke fara tabawa idan mun Farka
📱Wasu su kwana da ita suna jin kida wasu kuma karatu
📱Wasu su farka cikin dare don kawai Suyi downloding Film amma ba don su yi Qiyamul Laili ba
📱Wasu kuma su raba dare suna chating ko browsing …. wanda hakan sai ya hana su tashi suyi sallar Asuba
📱Wasu kuma ko da yaushe suna “online” suna chating… Wani ma tun asuba idan ya hau sau tsakar dare zai sauka
Wani yana da Daruruwan Friends da yake chating da su… amma bai damu ya san halin da Yan uwansa na gida suke ciki ba…. Sai ya kebe kansa shi kadai a daki.
📱Wasu ana Idar da Sallah zaka ga sun dauko waya suna dannawa… sun manta da yin Adhkaar
Subhanallah… kai ka ce an yafe musu zunubansu da suka aikata.
📱Wasu idan hatsari ya faru maimakon su ceci mutanen sai su dauko waya su fara daukar hotuna
📱Wasu idan akai gobara mai makon su kai agaji sai su fara daukar hoto da wayoyin su suna posting… wataqila ko dan su samu comments
📱Wasu da anyi rasuwa sai a fara posting mai makon a fara yin abin da yafi dacewa ga wannan mamacin
📱 Wasu kuma ko me sukeyi ko kuma ko ina za su je sai sunyi posting
📱📱Wayoyin mu sun gama zame mana jiki
Wasu har chating suke a masallaci
Wasu a abin hawa cikin mota da sauransu
Wasu a dakin Jarabawa
Subhanallah… Wasu har kallon Film suke a masallaci …. Wannan wace irin Fitina ce wannan Al ummah muke fuskanta
Wasu ma suna tafiya a kan hanya suna danna wayarsu … sai sun kauce wa hatsari da kyar ko su zame ko ma su fada kwata
Wasu idan sukayi baqi sai kyale su saboda sun maida hankalinsu kan wayarsu
Wasu kuma Ma’auratan basu da lokacin junansu saboda sun sa waya a gaba
Abin mamaki… Wasu ma idan suka zo sallah sai su karanta Suratul Asr domin su gama da sauri don su cigaba da harkokinsu da Wayarsu… Basu san ma cewa Suratul Asr tana magane akan amfani lokaci wajen aikin kwarai ba
Mafi yawancin wasu wayoyinsu suna sanya Su su zama munafukai… Wasu kuma wayoyinsu za su kaisu wuta basu sani ba
Wasu saboda waya sai su zama na qarshe wajen zuwa masallacin Juma’a kuma su ruga kowa dawowa da an Idar
Wal’iyaazubillah!!!
Sheikh Muhammad Saleh Al Uthaymin (Allah yayi masa Rahama) yana cewa:
Duk wanda baya amfani da Lokacin sa wajen yin aiki na Da’a da neman yardar Allah… To abinda yafi dacewa da shi ko kuma ya fiye masa sauqi shine MUTUWA.
DARASI : Abinda ya kamata mu Fahimta daga wannan Naseeha shi ne; Wayoyin da muke amfani da su … Mafi yawancin su Yahudawa ne suke Qera su … kuma suna da Manufar Shagaltar da mu domin Mu manta da Asalin dalilin da yasa Allah ya halicce mu, kamar yadda Allah SWT ya fada:
Ban Halicci Aljanu da Mutane ba Face domin su Bauta Min (surah ta 51 aya ta 56)
Saboda haka suna so mu shagala mubar ibada da sauran Ayyukan Da’a ga Allah.
Sannan za ka samu yawancin mu masu amfani da waya tana sa muna aikata sabo.
Ina fatan Allah ya shiryeni ya shiryeku ya Gafarta mana.