Ads

HAKKIN MIJI AKAN MATA DA HAKKIN MATA AKAN MIJI

0

- Advertisement -

HAKKIN MIJI AKAN MATA DA HAKKIN MATA AKAN MIJI

Alummarhausa.com.ng

AN kasa hakkokin maaurata zuwa kashi uku
1⃣na daya hakkin miji akan mata
2⃣na biyu hakkin mata akan miji
3⃣na uku hakkin tarayya tsakanin maaurata

Hakkin mata akan miji sune:

Related Posts
1 of 9

1.ciyarwa gwargwadon iko.
2.tufatarwa daidai iko.
3.shayarwa.
4.kayan kwalliya.
5.kayan tsafta.
6.gurin kwana.
7.kula da lafiya.
8.hakkin saduwa.
9.ilmantarwa.
10.girmamawa.
11.mutuntawa.
12.tausasawa.
13.yabawa ga abinci ko kwalliya ko tsafta.
14.nuna damuwa da ita.
15.sakar mata fuska da murmushi.
16.gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.
17.zama hira da tattaunawa da ita.
18.kiranta da suna mai dadi.
19.yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.
20.fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.
21.taimaka mata aikin gida ko dan kadan.
22.bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.
23.bata damar zabin tufafin da zata sauya.
24.mutunta iyayenta da danginta.
25.A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.
26.A yaba mata idan tayi daidai.

Alummarhausa.com.ng

  1. kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
    28.banda duka.
    29.banda zagi.
    30.banda saurin fushi.
    31.ka zama miji mai tsafta.
    32.ka zama miji mai kula da goge baki.
    33.miji mai kwalliya.
    34.miji bamai almubazzaranci ba.
    35.miji bamai mai kwauro ba.
    36.miji bamai shan taba ba.
    37.miji bamai mai shan giya ba.
    38.miji bamai yawon dare ba.
    39.miji bamai neman mata ba.
    40 Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalansa.
    41.miji mai yawan fada.
    42.kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyali.
    43.kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalansa suke ciki.
    44.kada ka zama miji mai tsananin kishi.
    45.kada ka zama miji mai yawan zagi.
    46.ka nuna wa matarka cewa gamsu da yanayinta.
    47.ka bata dama ta fadi raayinta.
    48.kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.
    49.ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.
    50.yin wanka tare a wasu lokuta.
    51.rera mata waka da kirari.
    52.yin wasa da guje-guje.
    53.kada ya zama miji mai zargi.
    54.kada miji ya zama mai mugunta.
    55.kada miji ya zama mai kushe.
    56.kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.
    57.kada miji ya zama mai ragwanci.
    58.mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
    59.miji ya zama mai kaunar yayansa.
    60.miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa Na biyu hakkin miji akan mata sune:

1.Ta rike masa amana,

  1. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane.
  2. Ta kula da dukiyarsa
  3. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya
  4. TA girmama shi a gaban idansa
  5. TA kare girmansa a bayan idansa
  6. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a wajenta
  7. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta
  8. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.
  9. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi
    11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .
    12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi
    13.Idan ya bata kadan taga yawansa
    14.Idan ya bata da yawa tayi godiya
    15.Ta farka daga bacci kafin ya farka
    16.Sai yayi bacci kafin tayi
    17.Tayi hakuri idan yayi fushi
    18 Tayi taushi idan yayi tsauri
    19.Ta lallashe shi idan ya hasala
    20.kada ta nuna raki a gabansa
    21.kada tayi kuka alhali yana dariya
    22.kada tayi dariya alhali yana kuka
    23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu
    24.kada ta matsa masa da bukatu
    25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida
    26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai
    27.kada ta dinka kushe tsarinsa
    28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta
    29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta
    30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau
    31.Ta dinka boye abu mummuna
    32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake shi ya warware ta
    33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina
    34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa
    35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki
    36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya
    37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako
    38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu
    39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin da ya dawo
    40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi
    41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta
    42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge
    43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro
    44.Tayi ado karshen iyawarta
    45.Ta bayyana halaye masu kyau
    46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai
    47.Ta bayyana kanta a matsayin mace
    48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
    49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta
    50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so
    51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna
    52.Ta yafe masa idan ya munana mata
    53.Ta karbi uzurinsa
    54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa
    55.kada ta dau azumi sai ya sani.
    56.kada ta fita daga gida sai ya sani.
    57.Ta iya girki kala-kala.
    58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula.
    59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni.
    60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai

Na uku shine hakkokin tarayya tsakanin maaurata

1 Nunawa juna kauna da soyayya
2 Tarayya da juna cikin abinda ya sami dayan ko na farin ciki ko bakin ciki
3 kowa ya dinka yiwa abokin zaman sa kwalliya da tsafta.
4 kowa tsakanin maaurata ya zama mai kishin da uwansa
5 a sami amincewa juna
6 kowa ya bawa kowa daga cikin hakkin jin dadi da juna ta hanyar da shari’a ta amince.
7 kyakyawan zamantakewa tsakanin juna
8 hakuri da juna9 Amincewa juna
9 Farantawa juna rai.
10 su zama kamar abokan juna da yin shawara da juna
11 Nuna juna kauna daga bangaran kowa daga cikin su.
12 Girmama iyayan da yan uwan juna
13 Taimakon juna a lokacin da wani daga ciki ya gamu da jarrabawa.
14 Wani su dinka tona asirin juna a waje
15 Banda cin Amanar juna.
16 kada su dinka bayyana wani mu’amalar su ta auratayya.
17 Akwai gado a tsakanin su idan daya daga cikin su ya fara rasuwa.
Wannan sako ne ga dukkan maaurata su zauna suyi nazarin wannan sako kowa yaga abinda yake yi a ciki, domin mu gudu tare mu tsira tare
Allah ya bamu ikon kiyaye hakkin juna.
YA cika zukatan mu da kauna da soyayya da girmamawa tsakanin mu da iyalinmu.

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.