Wasu jigogi a gwamnatocin Amurka da Burtaniya da Australia sun nuna damuwa dangane da shirin kamfanin shafin Facebook na hana kutse a cikin sakonnin da ake aikawa ta shafukansa, suna cewa hakan zai iya shafar harkar tsaro.
Cikin wata wasika, babban lauyan gwamnatin Amurka da ministocin cikin gida na Burtaniya da Australia sun bukaci shugaban kamfanin na Facebook, Mark Zuckerberg, da ya dakatar da shirin kange sakonnin da ake turawa a kafofin intanet mallakarsa ciki har da Facebook din, ta yadda sai wanda mai aika sako da wanda aka tura masa ne kadai za su iya karantawa, ko gani.
Sun jaddada cewa kange sakonnin zai yi cikas ga kamfanonin fasaha wajen gano miyagun ayyuka da taaddanci.
Sai dai kuma kamfanin na Facebook ya ce ma
abota dandalin da dangoginsa suna da hakkin sirri dangane da irin tattaunawar da suke yi ta intanet.
Wasikar manyan jami’an ga shugaban na Facebook kan ya dakatar da wannan aniya tasa da ya shirya yi a dukkanin kafofi ko shafukan inatenet da ke karkashinsa, suna nuna fargaba da damuwarsu ne kan yadda hakan zai zamar musu ko hukumomin tsaro wani shinge ko katangar karfe da ba za su iya ratsawa ba, domin bincike kan wani sako ko sadarwa da suke zargi a kai.
Sai dai yayin da suke nuna wannan damuwa su kuwa masu rajin kare sirri maraba suke da matakin da cewa, ko ba komai zai kara inganta tsaron kowa.
Tsarin dai na nufin ko da hukumomin tsaro sun gabatarwa kamfanin na Facebook takarda ta izinin samun wasu bayanai kan wani sako, shi kansa kanfanin ba zai iya taimakawa ba.
Wasikar ministocin ta yi gargadin cewa shirin zai hana kamfanonin sadarwa daukar mataki a kan sakonni ko abubuwan da suka saba doka, kamar hotunan lalata na cin zarafin yara, da abubuwan ta`addanci, wanda hakan zai jefa ‘yan kasa da al’umma cikin hadari a cewarsu.
Yayin da jami’an kasashen uku ke wannan fafutuka, mai magana da yawun kamfanin na Facebook, jaddada matsayarsu ya yi a kan matakin na tabbatar da kariya ga sirrin ma’abota shafin da dangoginsa mallakin kamfanin.
Ya ce sun yi amanna jama’a suna da ‘yancin samun sirri a tattaunawarsu ta intanet, a duk inda suke a fadin duniya, amma kuma ya ce suna mutuntawa tare da tallafa wa aikin jami’an tsaro na tabbatar da kare lafiyar mutane.
A kan hakan ne ya ce suna tattaunawa ta kut da kut da kwararru a fannin kare lafiyar yara, da gwamnatoci da kamfanonin sadarwa, inda suke kokarin samar da wasu sabbin rukunan jami’ai da fasaha ta yankan-shakku domin tabbatar da tsaron jama’a, in ji shi.