Kurkum Kurkum (turmeric) amfani da shi wurin sanya abinci ya yi kamshi da kuma dandano ba ne, a’a, ana amfani da shi wurin gyaran fata.
An fara amfani da Kurkum wajen rinin tufafi ne, daga baya aka fara amfani da shi wurin girki a Indiya. Har yanzu ana amfani da kurkum yayin bukukuwa a Indiya saboda launinsa.
A Kudancin Indiya ma akan yi amfani da shi wurin yi wa amarya ado, inda ango yake shafa mata a wuya. Amare a Indiya sukan shafa kurkum a jikinsu don gyaran jiki.
A Najeriya kabilar Kanuri da Shuwa daga kasar Barno sukan yi amfani da kurkum wurin gyara wa amare fata don su samu fata mai laushi da haske da kuma kamshi..
Kurkum kan magance kurajen fata da kaushin fata da tabon fata da kyesbi da kuma sauran cututtukan fata.
Yakan taimaka wurin magance yaushi da jemewar fata, sannan na sanya fata haske da kuma taushi. Na kuma kare jiki daga illar hasken rana.
Yadda ake hadawa:
- Ki hada cokali 4 na hodar kurkum da jus din lemon tsami da kuma ruwan gurji a cikin kwano ko roba.
- Daga nan ki zuba cokali 3 na nono ko kuma danyar madara.
- Sai ki zuba ruwan dumi, sannan ki rika gaurayawa har sai hadin ya gaurayu sosai.
- Daga nan ki shafa a jikinki zuwa awa daya.
- Wanke jikinki da ruwan dumi, sannan ki tsane da tawul mai tsabta.