FADAKARWA: ABOKIN HIRA 3
Wanda ya Kunshi Labarai Masu Nishadantarwa Tare da Fadakarwa
Darasi na 3
Darasin namu na yau shine Fushin Alqali
Wani Alqali ne ya samu hatsaniya tsakanin sa da matarsa tun da safe.
Ya fito daga gidansa a fusace, ya isa kotu. Zaunawar sa ke da wuya sai Mufti ya karanta masa qara ta farko yana cewa:
Allah ya dade ran Alqali, qara ta farko a yau ita ce ta wata mata da take qarar mijinta ya mare ta.
Sai Alqali ya yi wuf ya ce, ya mari banza!
Darussa:
- Mata sai a hankali
- Ba a yanke hukunci a cikin fushi
- Ba kowace matsala ake kai Kotu ba
- Duk halin da kake ciki akwai dubu irin ka