Ads

FADAKARWA: ABOKIN HIRA 4

0

- Advertisement -

Alummarhausa.com.ng

Wanda ya Kunshi Labarai Masu Nishadantarwa Tare da Fadakarwa_

Darasi na 4

Related Posts
1 of 9

Darasin mu na yaushine Rama Cuta ga Macuci

An yi wani Alqali a garin Kufa mai tsananin kaifin basira da hankali ana ce da shi Ibnu Abi Laila. Watarana wasu mata suka je wurin sa suna koke a kan sha’aninsu.

Sai ya ce masu wace ce za ta fara magana a cikinku? Sai dayarsu ta ce da daya ki fara gabatar da kararki. Ta ce, Allah ya taimaki Alqali, mahaifina ya rasu wannan kuma kanwarsa ce, kuma ita ce ta yi raino na har na girma.

Alqali ya ce, to mene ne matsalarki da ita? Ta ce, wani dan uwana ne ya zo dan baffana ya nemi aure na kuma ta amince ta aurar da ni gare shi. Bayan shekaru uku da ta lura da halin kirkinsa sai ta qawata masa diyarta har ta ba shi sha’awa ya nuna son ta, sannan ta nemi ya aure ta bisa sharadin ya sanya al’amarina a hannunta. A ranar da zai tare da diyarta sai ta ce mini kawai ki fara idda domin na sake ki bisa izinin mijinki.

Allah ya taimaki Alqali ana cikin haka, ina zaune a gidanta sai mijinta ya dawo daga tafiya, sai na yi ma shi ado mai ta da hankali har ya yi sha’awa ta.

Sai na ce masa, idan kana so zan aure ka amma da sharadin ka sanya al’amarin gwaggota a hannuna. Nan take sai ya amince. Ni kuma ban bata lokaci ba na kira ta na ce, sai ki fara idda domin na sake ki bisa izinin mijinki, kuma na aure shi.

Alqali ya ce, to ai shikenan; kin rama.

Muhimman Batu
1 of 2

Alummarhausa.com.ng

Ta ce, Allah ya taimaki Alqali, yanzu maigidan nan nawa ya mutu kuma gwaggota tana neman in ba ta gadonsa. Alqali ya ce, ta ina kuma za ta gade shi? Ta ce, abinda ya faru shi ne, bayan da mijina ya cika, kuma na gama idda sai gwaggota ta zo da surukinta wanda yake tsohon mijina ne ta ce, ya yi muna hukunci a kan sha’anin gadon da tsohon mijinta ya bari. Da ya zo muka hada ido da shi sai tsohuwar soyayyarmu ta motsa, muka tuna baya. Sai ya qyalla idonsa ya nuna min buqatarsa, sai na kebe da shi na ce masa, zan sake aurenka da sharadin ka sanya igiyar auren matarka a hannuna. Ya kuwa amince, don haka sai na sake ta. Alqali ya saki baki yana jin wannan ikon Allah.

A nan ne fa sai daya matar wadda take gwaggonta ta kada baki ta ce, Allah ya taimaki Alqali yanzu ka ji labarin abinda yake tafiye da mu. Wannan shegiyar diya ta tsinke igiyar aurena da na diyata sannan kuma ita za ta ci gadon mijina?

Alqali ya bushe da dariya. Ya ce, to ya aka iya ne? Wanda ya haqa ramin mugunta idan ya fada a ciki wa zai zarga?

Darussa:

  • Idan za ka gina ramin mugunta gina shi gajere.
  • Idan ba ka da kunya sai ka yi abinda ka ga dama.
  • Idan dattijo bai ji kunyar hawan jaki ba, jaki ba ya jin kunyar kayar da shi
  • Hattara da kaidin Mata
  • Shin wanne darasi ka koya a wannan labari

Don Allah Katura zuwa daya dga cikin social media dake don wasu su amfana

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.