Ads

Don Neman Zama Marubuci

- Advertisement -

Tsarukan Aiki A Shafin AlummarHausa

Alummarhausa.com.ng

Shafin AlummarHausa shafi ne dake kawo Tarihin Kasar Hausa da kewayanta, gami da tarihin wasu Al’adun a yankin mu na Africa bugu da kari da samar da sahihan maganin gargajiya namu na Hausawa don magance cututtukan dake damun mu.

Don haka wannan shafin yake neman Kwararrun Marubuta daga kowane bagare na shafin domin yin aiki a shafin, kuma a biyashi duk wata.

Sharuddan Zama Marubuci

Da farko, marubuci ya tabbatar cewa Tarihin da zai bayar shi ne ya rubuta, ko kuwa shi yake da hakkin mallakar Tarihin ko ma duka biyu.

Dole Tarihin ya kasance sabo ne, ba a taba buga shi a wata kafa ba, (Yanar Gizo). Koda ya kasance an buga to a tabbatar da cewa bayanan ciki rubutun ya banbanta da wadancan.

Dole marubuci ya tabbatar da Hotunan da zai amfani dasu yana da Hakkin Mallakar su, ko kuma ya same su a wuraren da ake samar da hoto kyauta kamar su Pixabay. Za’a iya tutubarmu don mu samarwa da rubutun ka Hoto.

Dole Tarihin da zaka bayar kada ya gaza a kalla kalmomi dari Shida (600 words) zuwa sama.

Da zarar an shiga wannan  yarjejeniyar, marubuci ba zai iya wallafa wannan Rubutu nasa a wata kafar ba. Amma zai iya wallafa a kalla kalmomin da bazu kaza dari (100 wards) ba a shafinsa na kafafen sada zumunta, sai a kasan ya sanya link da za’a  taba don dawowa cikin shafin AlummarHausa a karanta cikakken rubutun.

Marubuci na damar  ya wallafa rubutu daga kowane bangare da AlummarHausa keda su, guda Uku (3) a Kullum.

Marubuci nada damar (tallata) Rubutunsa gwargwadon yadda zai zama dandano misali a kalla kalmomin da bazu kaza dari (100 wards) ba, a shafukansa na sada zumunta da duk wuraren da yake da makaranta inda yake sanya rubutunsa. Sannan ya saka link din da za’a samu cikakken rubutun, wato zuwa AlummarHausa don yasamu viewers sosai.

Alummarhausa.com.ng

AkummarHausa na da hakkin mallaka (copyright) na juya rubutun ka zuwa audio ko duk nau’in documents, ko ma buga shi a matsayin littafi a koda yaushe.

Sannan AlummarHausa na iya dorawa a duk kafafenta na internet ko kuma wurare da take tallata hajojinta.

TSARIN BIYAN KUDI

Tsarin biyan kudi ga marubuci zai iya zama duk wata.

Yada abin yake shine kamar haka:

Idan marubuci ya wallafa rubutunsa kuma ya samu mabiya Mutum Dubu (1000 View) suka karanta shi a cikin shafin Alummarhausa, to a wannan watan yana da ₦1,500. A tuntube mu idan ba’a fahimta ba.

ABIN LURA;

Biyan zai Fara ne a yayin da kasamu sama da 1000Views.

Alummar Hausa na iya Sabunta  wadannan ka’idoji/yarjejeniya a kowane  lokaci, gwargwadon juyawar zamani.

Karya daya daga cikin wadannan ka’idojin zai iya rushe baki dayan yarjejeniyar.

A Cike Wannan Form don sanin wane bangare ya kamata ka dauka.

Wannan shine bangaren da zaka zaba don gudanar da aikinka a shafin ALUMMAR HAUSA
Wannan tabayar anaso asan cewa shin kana aiki a wani shago na naura mai kwakwalwa wato (Computer).
Wannan tabaya ita kuma na nufin wanne lokaci kake dashi na yin Darasi (posting) a shafin.
Don Mu tabbatar da cewa zaka iya yin ruubutu da kanka
Bayani game dakai (munso ace kayi computer)

Alummarhausa.com.ng