Alummarhausa.com.ng

HIMMA BATA GA RAGO

Alummarhausa.com.ng

Alummarhausa.com.ng

ABOKIN FIRA

Wanda ya Kunshi Labarai Masu Nishadantarwa Tare da Fadakarwa

Alummarhausa.com.ng

DARASIN MU NA YAU MAI TAKEN HIMMA BA TA GA RAGGO

A birnin Andalusiya na qasar Spain aka yi wasu abokai matasa guda uku masu

dakon kaya a kan Jakuna. Watarana sun dawo daga aikin nasu suna hutawa sai daya daga cikinsu ya ce ma abokansa, ya kuke gani in da zan zama Sarkin Musulmi? Su biyu suka bushe da dariya, suka ce, me kuma ya hada dan dako da sarauta?! Abokin nasu ya dage sai sun fada masa burinsu idan Allah ya yi mishi sarauta, su kuma suna ta yi masa izgili.

A cikin raha da wasa daya daga cikin su ya ce, to, idan Allah ya sa ka zama Sarkin

Musulmi ka yanka mani gona mai fadin gaske, ka cika mani qatuwar jaka da kudin

Zinari, sannan ka ba ni kyautar bayi dari ‘yan mata. Amma na biyun sai ya ce, idan har ka yi sarauta ina son ka yi umurni a dora ni a kan Jaki a juya fuskata a zagaya da ni cikin gari ana shelanta cewa, ga Dujjal nan ya bayyana ku yi hattara da shi!

Sannan ya bushe da dariya.

Tun daga wannan rana, abokin nan nasu ya riqa iyo a cikin gulbin tunani, ta ya ya za ayi ya yi sarautar Sarkin Musulmi kuma shi ba dan gidan sarauta ba, ba ya

da alaqa ta kusa ko ta nesa da ita?! A qarshen nazarinsa ya fada ma zuciyarsa cewa,

dole ne ya sayar da Jakinsa domin ba a Sarki mai irin wannan sana’a. Nan take ya tafi kasuwa ya kai Jakinsa ya sayar da nufin ya yi bankwana da sana’ar dako har abada.
Bayan nazari mai zurfi sai ya shiga aikin ‘yan sanda. Saboda sabo da aikin wahala nan take ya yi fice a cikin tsararrakinsa, ya riqa samun qarin girma har Allah ya

hukunta ya zama shugaban ‘yan sanda na jiha, sannan na qasa baki daya.

A kwana a tashi Sarkin Musulmi Abdulmalik dan Marwana ya cika, aka nada

Dansa Hisham wanda bai wuce shekaru goma ba a wancan lokaci. Don haka aka yi matsaya a kan cewa, a sanya masa masu kula da shi da yadda yake gudanar da

sha’anin sarauta. Wadanda kuma su ne za su riqa magana da yawunsa kafin ya girma ya isa yin komai da kansa. Shugaban ‘yan sanda na daga cikin mutane uku da aka zaba don wannan aiki tare da Malam Mus’hafi da wani bawan Allah ana ce masa dan Abu Galib.

Da ya samu wannan dama sai ya nemi auren ‘yar gidan Abu Galib ya hada ta da

dansa don ya rufe bakin abokin aikin nasa ga duk abinda zai yi a nan gaba. Sannan ya riqa neman kusanci da Subhi mahaifiyar sabon Sarki. Da alaqarsu ta yi qarfi sosai sai ya hada kai da ita suka cire Mus’hafi daga cikin masu isar da umurnin Sarki. Da wannan ya zama shi kadai ne mai magana da yawun Sarki mai ci, sai kuma surukinsa

wanda tuni ya bi wasu hanyoyi da suka sa ya shiga gabansa.

Da aka cimma wannan matsayi sai ya fitar da wasu sababbin dokoki kamar

haka: Sarki ba zai qara fitowa a cikin jama’a ba sai da sanin sa, kuma babu mai isar

da saqonsa ga jama’a in ba shi ba. Sannan ya mayar da duk sha’anin sarauta a

gidansa, maimakon fadar Sarki. Sai ya fito kullum da safe ya saurari koke-koken

jama’a, ya tsara mayaqa, ya nada alqalai da sauran duk ayyukan da suka danganci

sarauta. Da haka ya zama shi ne Sarki na haqiqani mai wuqa da nama a hannunsa.

Kuma ma dai gaisuwar sarauta ake yi masa.

Duk abinnan da ake yi wannan bawan Allah kamar yadda bai manta kudurinsa ba, haka ne kuma bai manta da abokansa biyu ba. Bayan shekaru talatin da sayar da Jakinsa sai ga shi a kan gadon sarauta, Malamai da Limamai da Alqalai

sun kewaye shi, ga kuma asakarawa sun yi tsaitsaye a bayan sa, fadawa suna gefe

suna ta yi masa kirari. Ana haka sai ya kira wani dan sanda ya ba shi umurnin ya je ya nemo masa abokan nan nasa su biyu. Ya fada masa wurin da zai same su, suna can suna sana’arsu ta dako da suka saba. Ba su san abinda ya hada su da Sarki ba, ballai su san abinda Sarki yake kiran su a kan sa. Shi kuma wancan abokin sana’arsu sun dade da jefa shi a kwandon mantuwa, balai su yi tunanin ya zama ko Masinja ma balai Sarki. Da suka yi ido hudu da Sarki sai gabansu ya fadi, suka sunkuyar da kawunansu suna taslima a cikin zukatansu. Sarki ya tambaye su, ko kun shaida ni?

Suka amsa masa, Na’am. Allah ya taimaki Sarki ai mun dauka kai ne ba za ka shaida mu ba! Ya ce da su, kun tuna alqawarina da ku idan na ci sarauta? Suke ce eh, lallai

babu shakka ba mu manta ba. Ya ce, to ku maimaita a gaban jama’a kowa ya ji. Na

farkonsu ya fadi abinda ya roqa, aka ce nan take a zartar da buqatarsa. Jin haka sai

na biyun ya durqusa yana neman afuwa daga wurin Sarki. Sarki ya ce, sam. Dole ne sai ka fadi, kuma sai an zartas da abinda ka roqa domin kowa ya sani kuma ya yarda cewa, Allah shi ne gwanin sarki, kuma babu abinda yake iya buwayar sa. Haka kuwa aka yi. Aka dora wannan bawan Allah a kan Jaki aka zagaya gari da shi ana shelanta cewa, jama’a ga Dujjal ya bayyana kowa ya yi hattara da shi.

Wannan labari ba almara ba ce. Labarin gaskiya ne. Wannan bawan Allah da

ya zama Sarki sunansa Muhammad bin Abi Amir. Lamarin kuma ya faru kusan shekaru dubu daya da dari biyu da suka wuce. Littafan tarihi sun ruwaito shi.

Darussa:

  • Idan kana son cim ma nasara a rayuwarka dole ne ka yanka Jakin kasala da zaman banza da mafarkin cin nasara daga kwance. Ka tsara rayuwarka ta hanyar da za ka samu biyan buqata. Sannan ka dage, domin Zomo ba ya kamuwa daga kwance.
  • Kowane mutum ka gani akwai abinda Allah gwanin Sarki ya tsara masa. Sanin gaibu sai lillahi.

  • Ba a izgili da ikon Allah domin babu abinda yake gagarar sa.

⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com

Alummarhausa.com.ng

FadakarwaNishadantarwa
Comments (0)
Add Comment

Alummarhausa.com.ng